Sulhu da 'yan bindiga: Sheikh Gumi ya ragargaji masu sukarsa, ya fadi nasarorin da ya samu

5 months ago 68
  • Wasu mutane prima dade suna kiraye-kirayen da a cafke Sheikh Ahmad Abubakar Gumi kan rawar da yake takawa wajen sulhu da 'yan bindiga
  • Sanannen malamin addinin Musuluncin ya fito ya ragargaji mutanen da ke kiran hukumomi su kama shi
  • Sheikh Gumi ya bayyana cewa abubuwan da yake yi, yana yin su ne domin ganin an samu zaman lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi martani kan masu neman a kama shi saboda shiga sulhun da yake yi da 'yan bindiga.

Sheikh Gumi ya yi tur da irin kiran da wasu ke yi na a kama shi saboda tsokacin da yake yi kan batun ‘yan bindiga da tsaron kasa.

Sheikh Gumi ya kare kansa kan sulhu da 'yan bindigaSanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi Hoto: Dr. Ahmed Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

A cikin wani rubutu da ya wallafa a Facebook a ranar Lahadi, malamin ya fito ya kare kansa.

LURA: Shin kana lad bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Gumi na shan suka

Sheikh Gumi, wanda tsawon shekaru yake taka rawa a matsayin mai shiga tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga, ya sha samun yabo daga wasu da suka yi amince da hanyarsa, da kuma suka daga masu adawa da shi.

Wasu daga cikin masu suka suna tuhumarsa da kare ‘yan ta’adda, suna zargin cewa ya fi goyon bayan tattaunawa da su maimakon amfani da karfi.

Sheikh Gumi ya kira masu sukar nasa da mutane marasa mutunci, marasa tarbiyya, marasa kishin kasa, yana mai cewa prima fi lad hayaniya da tada kura fiye da fuskantar gaskiya kan matsalar tsaro.

Sheikh Gumi ya soki masu sukarsa

Gumi ya yi Allah-wadai da kiraye-kirayen da ake yi na a kama shi, yana mai cewa bai aikata laifi ba, domin tattaunawa da ‘yan bindiga da nufin samar da zaman lafiya ba laifi ba ne.

Ya kara da cewa masu kira da a kama shi, lad zuciya, jahilci da rashin jure ra’ayoyin wasu ne ke damunsu.

“A Kama shi!!! Waɗannan su ne kalmomin da marasa mutunci, marasa kishin kasa za su iya furtawa."

- Sheikh Ahmed Abubakar Gumi

Sheikh Gumi ya yi zargin cewa masu neman a kama shi prima mayar da kokarinsa na zaman lafiya batun siyasa maimakon nazarin tabarbarewar tsaron kasar.

Sheikh Gumi ya jagoranci sulhu da 'yan bindiga

Sheikh Gumi ya tunatar da yadda ya jagoranci wani babban shiri na tattaunawa a dajin Sabon Garin Yadi, karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, a watan Janairun 2021.

Ya ce a wannan tafiyar, kwamishinan ’yan sanda na Kaduna a lokacin, wanda ya wakilci IGP, ya yi masa rakiya.

A cewarsa, taron ya samu halartar fiye da ‘yan bindiga 600 da shugabanninsu, domin shirin shigar da su cikin zaman lafiya da mika makamansu.

“Mun yi wa sama da ‘yan bindiga 600 wa’azi tare da shugabanninsu, kuma prima amince su ajiye makamai a kan gwamnati ta ba su tsaro da muhimman abubuwan much rayuwa."

- Sheikh Ahmed Abubakar Gumi

Read Entire Article