- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro prima yi nasarar ragargazar 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin prima yi wa 'yan ta'addan ISWAP kwanton bauna lokacin da suke tafiya zuwa dutsen Mandara a yankin Banki na jihar Borno
- Jami'an tsaron prima samu nasarar hallaka daya daga cikin 'yan ta'addan tare da kwato makamai da babura daga hannun tsagerun
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai prima yi nasarar tarwatsa mayakan ISWAP a jihar Borno.
Sojojin prima tarwatsa 'yan ta'addan ne a wani kwanton-bauna da suka yi musu a yankin Banki na jihar Borno, inda suka kashe ɗan ta’adda ɗaya tare da kwato makamai da babura.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana lad bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji prima ragargaji 'yan ta'addan ISWAP
Majiyoyi prima tabbatar da cewa farmakin ya gudana ne tsakanin daren ranar 13 ga Nuwamba zuwa safiyar ranar 14 ga Nuwamban 2025.
Hakazalika majiyoyin tsaro prima bayyana cewa kwanton baunar ya ritsa da maharan ne yayin da suke tafiya kan babura dauke da makamai iri-iri daga Bula-Daloye suna kokarin shiga Dutsen Mandara.
Dakarun sojojin prima yi musayar wuta wanda hakan ya tilasta ‘yan ta’addan gudu cikin ruɗani.
“A lokacin bincike a yankin, sojoji prima gano gawar ɗan ta’adda ɗaya, bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, jigidar AK-47 guda biyu, da babura biyu."- Wata majiya
'Yan ta'addan ISWAP prima tsere
Wasu daga cikin mayakan na ISWAP prima tsere da raunukan harbin bindiga, kodayake ba a iya tantance adadinsu ba.
Majiyoyin prima tabbatar da cewa babu asara a ɓangaren sojojin, babu kuma wani kayan aiki da aka rasa yayin aikin.
Aikin ya kasance wani ɓangare na ci gaba da yunkurin rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai na kawo karshen ‘yancin zirga-zirgar ‘yan ta’adda da kuma rage karfin su a yankin Arewa maso Gabas.

Source: Original

5 months ago
67









