Abduljabbar: Sowore ya fadi abin da ya sa ake tsare da malamin, ya sha alwashi

5 months ago 68
 Sowore Ya Fadi Abin da Ya Sa Ake Tsare da Malamin, Ya Sha Alwashi
  • Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya koka kan cigaba da tsare fitaccen malamin addini a Kano bayan laifin batanci
  • Ya bayyana cewa tun da dadewa ya yi niyyar kai wa malamin ziyara a kurkuku, amma hakan bai samu ba, abin da ya kira abin takaici
  • Sowore ya yi kira da a kawo ƙarshen duk wani nau’in danniyar addini a Najeriya, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi a mutunta ‘yancin kowa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fitaccen dan gwagwarmaya a Najeriya, Omoyele Sowore ya tabo batun ci gaba da tsare Malam AbdulJabbar Kabara da ake yi.

Abduljabbar na ci gaba da zama a gidan kaso ne bayan tuhumarsa da kalamai marasa dadi ga fiyayyen halitta Annabi SAW.

Sowore ya soki hanyar da aka bi aka tsare AbduljabbarMalam Abduljabbar Kabara da Omoyele Sowore. Hoto: @YeleSowore.
Source: Twitter

Sowore ya soki ci gaba da tsare Abduljabbar

Sowore ya bayyana haka ne a yau Lahadi 16 ga watan Nuwambar 2025 a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter.

LURA: Shin kana lad bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan gwagwarmayar ya ce abin takaici ne har yanzu a ce ana tsare da malamin duba da dalilin da ya sa aka daure shi a gidan gyaran hali.

Sowore ya ce ya kamata ya kai masa ziyara tun tuni a kurkuku amma hakan bai samu ba inda ya ce lamarin abin takaici ne.

Bukatar Sowore crippled da tsare Malam Abduljabbar

Ya bukaci kawo karshen danniya a bangaren gudanar da addini inda ya zargi cewa an hukunta Malam Abduljabbar ne saboda bambancin akide da wasu malaman Kano.

A cikin rubutunsa, Sowore ya ce:

“Yaya batun ‘yanci da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya dade haka? Ya kamata successful kai masa ziyara a kurkuku tun tuni, tabbas wannan abin bakin ciki ne."Abin takaici ne cewa har yanzu malamin addini yana tsare saboda kawai fahimtarsa ko tafsirin da yake yi ya bambanta da na malamai da masu mulki a Jihar Kano ke tare da su."Lokacin kawo ƙarshen danniyar addini a Najeriya ya yi, yanzu."
Sowore ya tsoma baki kan lamarin AbduljabbarDan gwagwarmaya a Najeriya, Omoyele Sowore. Hoto: Omoyele Sowore.
Source: Facebook

Marta...

Read Entire Article